Rasha ta fadada ikonta a yankin Pasifik
September 7, 2012Tun kusan shekaru 20 da suka gabata ne dai wannan yanki ya kama hanyar samun bunkasar tattalin arzikin da Rasha ke son cin moriyarsa.A wani taron da kasashen APEC suka gudanar domin duba hanyoyin bunkasa tattalin arzikinsu a birnin Vladiwostok na Rasha da ke yankin na Pasifik, Putin ya yi misali da aike fasahar kasarsa domin yin amfani da ita wajen gina tashohin nukiya a China. Shugaban na Rasha ya kuma yi kira ga kasashe mambobin kungiyar APEC guda 21 da sun yi aiki tare domin kare kasuwanninsu daga abin da rikicin kudin euro ka iya haifarwa akansu. Ya ce har yanzu ba a samu bakin zaren warware rikicin tattalin arziki da ke addabar duniya ba.
Wannan taro ya samu halartar shugabanni cikinsu har da Hu Jintao na China da sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hilary Clinton da ta wakilici kasarta. Su dai kasashen APEC guda 21 sune ke mallakar kashi 44 daga cikin dari na kasuwancin a duniya da kuma kashi 54 daga cikin dari na tattalin arzikin duniya baki daya.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe