1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta gargadi Amirka a kan Ukraine

Zainab Mohammed Abubakar
September 15, 2022

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce idan Amirka ta yanke shawarar bai wa Kyiv makamai masu linzami da ke cin dogon zango, za ta "shige gona da iri" tare da zama bangaren rikicin.

Russland Maria Sacharowa, Sprecherin des Außenministeriums
Hoto: Russian Foreign Ministry/REUTERS

A hirarta da manema labaru, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta ce, Rasha na da 'yancin kare yankunanta. Washington dai ta aika wa Ukraine makaman rokoki da za a iya harbawa zuwa nisan kilometa 80, amm har yanzu ta ki bayyana shirinta na aikewa da wasu makaman da ka iya ninka wannan tazarar idan an harba.

Sai dai jami'an Amirka sun ce Ukraine ta yi alkawarin cewar, ba za ta yi amfani da makaman rokokin da Washington ta bata wajen kai hari a yankunan Rasha ba. Mahukuntan na Kiev sun nemi agajin makamai kuma sun samu daga Amirka da kasashen Turai, domin abun da suka kira "taimaka musu wajen kariya" daga hare-haren dakarun Rasha.