Rasha ta janye daga yarjejeniyar dakarun turai
November 30, 2007Shugaban Rasha Vladmir Putin ya sanya hannu kann wata doka ta janyewar Rasha daga wata yarjeneiya ta kafa rundunar haɗin kai a turai da ake ganin muhimmi ne ga tsaron nahiyar.Yarjejeniyar ta 1999 ta ƙayyade yawan manyan makamai da za a girke a tsakanin tekun Atlantica da tsaunaukan Urals.Wannan doka da Putin ya sanyawa hannu ya nuna cewa nan gaba Rasha ba zata sake amincewa rundunar tsaro ta NATO yin bincike a gurarenta na soji ba.Gwamnatin Rasha tace ta ɗauki wannan mataki ne don nuna adawa da shirin Amurka na kafa tashar kariya ga makamai masu linzami a kasar Poland da Jamhuriyar Czech.Wannan sanarwar ta zo ne `yan kwanaki kaɗan kafin zaɓen majalisar dokoki ta Rasha.
A halinda ake ciki kuma ƙungiyar ta NATO ta roƙi Rasha da kada ta yi zagon ƙasa ga wannan muhimmiyar yarjejeniya da aka kafa tun zamanin tsohuwar Taraiyar Soviet.