1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Janyewar Rasha daga Kherson

November 10, 2022

Rundunar sojojin Rasha ta ce ta fice daga birnin Kherson na Ukraine da ta mamaye watanni biyun da suka gabata, a daidai lokacin da Amirka ta kiyasta cewa Moscow ta yi asarar dakaru sama da dubu 100 a yakin na Ukraine.

Ukraine | Kherson | Yaki | Rasha
Birnin Kherson na Ukraine, na daga cikin birane da yaki ya ragargazaHoto: Wolfgang Schwan/AA/picture alliance

Rundunar sojojin Rashan dai ta ce janyewar da take son yi daga birnin na Kherson, wata dabara ce ta yaki da za ta taimaka mata kare rayukan sojojinta. Da yake sanar da dalilansu na janyewar, babban jagoran dakarun Rashan a rikicin Ukraine Janar Sergei Surovikin ya ce sun lura samar da abinci da kayan aiki ga dakarunsu a birnin da ke kusa da teku na neman ya zama jidali. Mataki mai tsauri da su kansu dakarun Rasha suka amince sun dauka na ficewa daga wannan birni da ke zama birni mafi girma da suka mamaye tun bayan fara yakin na Ukraine, na nuna cewa sojojin na Rasha sun samu koma-baya a yakin a cewar masana. To sai dai rundunar sojojin Ukraine ta ce matakin na Rasha bai zo mata da mamaki ba, a ta bakin mai magana da yawun sojojin Ukraine din Natalia Gumeniuk.

Sojojin Ukraine, sun yi karin haske kan janyewar Rasha daga KhersonHoto: Ashley Chan/Imago

#b#Zuwan lokacin hunturu da kan sanya ganyen bishiya bushewa tare da sauya kala daga kore zuwa ja, wanda a lokacin da yake koren sojoji ka iya boyewa a cikinsa na daga cikin dalilin da suka sanya sojojin na Rasha sallama birnin na Kherson a cewar sojojin Ukraine. To sai dai kuma duk da haka a jawabin da yake a kowane dare, Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine ya gargadi sojojin kasarsa da su yi hattara. A hannu guda yayin da Rasha ke cewa ja da baya ga rago ba tsoro ba ne shirin fada ne, ita kuma Ukraine ke bugun kirjin tsoro ne ya kori Rashan shugaban Turkiyya Reccep Tayip Erdogan ya bayyana cewa janyewar Rasha daga Kherson mataki ne mai muhimmanci a kokarin da Turkiyya ke yi na sasanta hukumomin Moscow da Kyiv da suka kwashe fiye da watanni takwas suna gwabza fada a tsakaninsu.