Rasha ta janye na wucin gadi daga yarjejeniyar nukiliya
February 21, 2023Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ci alwashin ci gaba da yaki a Ukraine a wani gagarumin jawabi da ya yi wa yan majalisar dokokin Rasha da manyan kwamandojin soja.
Jawabin da ya kan yi wa al'ummar kasar duk shekara ya zo yayin da ake dab da cika shekara daya da yakin da Rasha ta kaddamar a kan makwabciyarta Ukraine.
Putin ya sanar da cewa Moscow za ta janye na wucin gadi daga muhimmiyar yarjejeniyar takaita makaman nukiliya tsakanin kasarsa da Amurka.
"Yace na sanar da cewa Rasha za ta dakatar da kanta daga aiki da yarjejeniyar makaman nukiliya kuma ba za ta shiga cikin sabuwar yarjejeniya a nan gaba ba."
A jawabin da ya shafe sa'oi biyu yana gabatarwa, Putin ya ce Rasha a shirye ta ke ta cigaba da gwajin makaman nukiliya idan Amurka itama ta yi hakan, matakin da ake gani ka iya kawo karshen yarjejeniyar dakatar da gwajin makaman nukiliya da aka samar tun lokacin yakin cacar baka.
Putin ya zargi Amurka da kawayenta na NATO da nuna muradunsu karara ta ganin gazawar Rasha a Ukraine.
Yarjejeniyar takaita makaman nukiliyar tsakanin Rasha da Amurka an sanya mata hannu a shekarar 2011 akan kuma tsawaita ta a 2021. Yarjejeniyar za ta kare ne a shekarar 2026.