Rasha za ta fara amfani da wata sabuwar doka
June 4, 2018Talla
Dokar wacce 'yan majalisar dokokin kasar suka kirkira tun bayan da kasar Amirka ta sanyawa Rasha takunkumi cikin watan Afrilun wannan shekara, a halin yanzu ta sahalewa shugaban kasar damar dakatar da alaka tare kuma da haramta cinikayya da dukkan kasashen da suka samu tsamin dangantaka da Rasha a kowanne lokaci.
Dangantaka ta kara tsami tsakanin Rasha da Amirka sakamakon musayar yawu kan rikicin kasar Siriya da kuma batun mutuwar wani tsohon jami'in hukumar leken asirin Rasha a kasar Birtaniya.