1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Duniya na Allah-wadai da hare-haren Rasha a Ukraine

October 10, 2022

Shugaba Vladimir Putin ya tabbatar da labarin hare-haren da ya kaddamar kan Ukraine yana mai cewa martani ne ga kasar da ta addabi Mosko da ta'addanci.

Rasha ta kai hare-hare da makamai masu linzami a UkraineHoto: Gleb Garanich/REUTERS

Mutum akalla goma ne suka mutu a sakamakon wasu jerin hare-hare da makamai masu linzami da Rasha ta kaddamar a wannan Litinin a wasu muhinman yankuna da ke Ukraine, rahotanni na cewa fararen hula da dama hare-haren suka rutsa da su. Shugaba Vladimir Putin ya tabbatar da labarin, inda ya ce, martani ne ga wadanda ke addabar iyakokin kasar da hare-haren da ya kamanta da na ta'addanci. Rahotanni sun kiyasta cewa hare-hare kimanin tamanin da uku sojojin Rasha suka kai da makamai masu cin dogon zango a yankuna masu mahinmanci a sassan kasar Ukraine. 

Wannan batun ya janyo martani daga shugabanin duniya inda Shugabar hukumar zartarwa ta Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce, Rasha ta kara tabbatar wa duniya cewa zalunci ta saka a gaba, a na ta bangaren kuwa, Kungiyar Tsaro ta NATO ta bakin shugabanta Jens Stoltenberg, ita ma ta yi Allah-wadai da hare-haren da ta ce an kai kan fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba. Gwamnatin Indiya ta nemi a gaggauta kawo karshen hare-hare a cikin wata sanarwa da ta fitar jim kadan da kaddamar da hare-haren.