1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai hari gabar kogin Bahar Aswad

Abdullahi Tanko Bala
July 26, 2022

Rundunar sojin Ukraine ta ce Rasha ta kai hare hare da makamai masu linzami a gabar kogin Bahar Aswad kusa da tashar jiragen ruwan Odesa da ake fitar da hatsi zuwa kasashen waje.

Russischer Angrif auf Odessa, Ukraine
Hoto: State Emergency Service of Ukraine/Reuters

Rasha ta kai sabbin hare hare yankunan Ukraine a daura da kudancin kogin Bahar Aswad yankunan da suka hada da Odesa da Mykolaiv.

Sojojin Ukraine sun ce Rasha ta kai hare haren ne da makamai masu linzami da ke cin dogon zango.

A yankin Odesa harin ya lalata gine-gine a wasu kauyuka na gabar kogi yayin da a Mykolaiv hare haren suka fada wani wuri na rumbin ajiya duk da yarjejeniyar da aka cimma ta bada damar wucewa da hatsi daga Ukraine ta kogin Bahar Aswad.