Rasha ta kai hari cibiyar horas da sojin Ukraine
March 13, 2022Talla
Ta kuma ce ta lalata tarin makamai da kasashen waje suka tallafa wa Ukraine da su. Sai dai kuma gwamnan yankin Maksym Kozytskyy ya ce mutane 35 ne suka mutu yayin da wasu 134 suka jikkata a harin.
Kakakin ma'aikatar tsaron Rasha Igor Konashenkov ya ce, Rasha ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da kai hari kan sojojin haya na kasashen wajen a Ukraine.