SiyasaUkraine
Rasha ta kai hari da makami mai linzami a Ukraine
December 25, 2024Talla
Mazauna birnin sun ce sun ji karar fashewar makamai, batun da ya haifar da rudani a wasu sassan birnin na Kharkiv.
Magajin garin birinin Ihor Terekhov ya ce Rasha ce ta kai harin kuma baya ga asarar ran da aka samu mutane da dama sun jikkata baya ga lalacewar gine-gine na fararen hula da aka samu sakamakon harin.
Ministan makamashi na kasar ta Ukraine ya ce wadannan sabbin hare-hare na Rasha sun fi mayar da hankali ne kan cibiyoyin samar da makamashi na kasar, a wani yunkuri da ya ce Rashan na yi na durkursar da fannin makamakin kasar baki daya.