Rasha ta kai hari gabashin Ukraine
January 15, 2023A sakon da ya wallafa a shafinsa na Telegram a wanna Lahadin, gwamnan yankin Valetyn Reznichenko ya ce, har kawo yanzu ana ci gaba da neman wasu mutane 40 da suka makale cikin baraguzan gine-gine.
Gwamnan ya kara da cewa an kafa tawagar ta mutane kimanin 550 da suka hada da jami'an 'yan sanda da na sa kai da kuma likitoci don binciko wa tare da ceton sauran mutane wanda suka yi batan dabo. Kawo yanzu dai an ceto mutane 39 daga gini baya ga mutane 73 da suka jikkata wanda a halin yanzu 12 daga cikinsu ke cikin halin rai kwa-kwai, mutu kwai-kwai.
Dakarun sojojin Ukraine sun ce an kai harin ne da makami mai linzami mallakin kasar Rasha, wanda Rasha ta sami nasarar jefa shi saboda Ukraine ba ta da isassun makaman da za ta kakkabo shi. Tuni dai shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine din ya mika sakon ta'aziyarsa ga 'yan uwan wadanda suka mutu.