1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar hari kusa da nukiliyar Ukraine

Abdullahi Tanko Bala
September 19, 2022

Ukraine ta ce Rasha ta harba makami mai linzami da ya fada kusa da tashar nukiliya ta biyu mafi girma a yankin Mykolaiv na kasar

Kernkraftwerk Süd-Ukraine
Hoto: Anatolii Stepanov/AFP

Wani hari da Rasha ta kai da makami mai linzami ya fada kusa da wata tashar nukiliya a kudancin Ukraine a wannan Litinin, sai dai rahotanni sun ce harin bai yi wa tashar nukiliyar wani lahani ba. Ukraine ta baiyana harin da cewa yunkuri ne na ta'addanci.

Harin dai ya fada tazarar mita 300 daga tashar nukiliyar inda ya haifar da wani wagegen rami da ya kai zurfin kafa goma sha uku a cewar kamfanin da ke kula da tashar nukiliyar Energoatom.

Ma'aikatar tsaron Rasha ba ta ce uffan ba a game da batun.