Rasha ta kai harin Zaporizhzhia
October 6, 2022Talla
Gwamnan yankin Oleksandr Starukh ya ce wasu mutane biyar sun makale cikin barakuzan gine-ginen. Harin na zuwa ne sa'o'i kalilan bayan da shugaban Ukraine Volodmyr Zelensky ya sanar da sake kwace iko da wasu kauyuka uku a yankin. Yankin na Zaporizhzhia da ke karkashin ikon Ukraine, na daga cikin yankuna hudu da Rasha ta shigar kasarta. A ranar Larabar da ta gabata dai, Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya rattaba hannu kan dokar da ke nuna cewa Moscow za ta karbe ikon tashar nukiliyar yankin.