1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai munanan hare-hare a kudancin Ukraine

Abdul-raheem Hassan ZUD
December 13, 2025

Harin jiragen yakin ya shafi tashoshin makamashin wutar lantarki a kudancin Ukraine, wanda ya shafi rashin wuta a sama da gidaje miliyan daya. Harin na cikin mafiya muni da ya shafi tashar jiragen ruwa na Odesa.

Shugaban aksar Ukraine, Volodymyr Zelensky
Shugaban aksar Ukraine, Volodymyr ZelenskyHoto: ODD ANDERSEN/AFP/Getty Images

Rasha ta kaddamar da sabbin hare-hare a tashar jiragen ruwa na Odesa da kewaye a kudancin Ukraine, hare-haren da suka faru cikin cikin dare, sun lalata tashoshin lantarki masu yawa wanda ya jefa rayuwar miliyoyin mutane a cikin duhu.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya yi ikirarin Rasha ta yi amfani da jiragen sama mara matuka guda 450 da makamai masu linzami guda 30 wajen kai mata farmaki, Ukraine ta ce wannan harin yana cikin munanan hare-haren da Rasha ta kai yankin Odesa tun bayan fara yakin mamaya tsawon shekaru uku.

Harin ya faru ne yayin da wakilin gwamnatin Washington ke shirin ganawa da Zelenskyy da sauran shugabanni a Berlin fadar gwamnatin Jamus don cimma matsaya kan shawarar samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha wacce Amurka ke jagoranta.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW