1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai sabon hari a kudancin Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
September 14, 2022

Sojojin Rasha sun harba makamai masu linzami guda takwas a kan wani birni na kudancin kasar Ukraine ba tare da salwantar da fararen hula ba.

Infografik Karte Lage in der Charkiw Region Ukraine EN
Taswirar bayanai game da halin da ake ciki a yankin Kharkiv na Ukraine

Hukumomin Ukraine sun zargi sojojin Rasha da harba makamai masu linzami guda takwas a birnin Kryvyi Rih na kudancin kasar, da nufin kawo cikas ga samar da ruwa a yankin. Sai dai a cikin wani sako da ya watsa ta yanar gizo, Kirill Timoshenko da ke zama babban jami'i a fadar shugaban kasar Ukarine, ya ce babu farar hula da ya jikkata a harin.

Sai dai shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya yi alkawarin cimma nasara a yakin da kasarsa ke yi da Rasha, a lokacin da ya ziyarci garuruwa da dakarunsa suka kwato daga hannun sojojin mamaya na Rasha. Idan za a iya tunawa dai, sojojin Moscow sun fuskanci koma- baya bayan da dakarun Ukraine suka yi amfani da motocin sulke da manyan makaman atilari wajen fatattakarsu daga Kharkiv a yankin Arewa maso gabashin kasar ta Ukraine.