1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai wa Ukraine hari sau biyu a jere

October 21, 2024

Jami'ai a Ukraine na cewa Rasha ta kaddamar da jerin wasu hare-haren jirage marasa matuka a Kyiv a karo na biyu a jere.

Hoto: Dnipropetrovsk Military Administration/Anadolu/picture alliance

A kalla jirage marasa matuka 10 ne Ukraine din ta ce ta kakkabo daga sassa daban-daban, inda fadowar baraguzansu suka haddasa lalacewar wasu rukumin gidaje da kuma raunata mutum daya kamar yadda magajin garin Kyiv Vitali Klitschko ya wallafa a shafinsa na Telegram. Hakan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Rasha ta kai hare-haren makamai masu linzami a birnin Kyiv da wasu biranen da suka yi sanadiyar jikkata mutane 17.

A gefe guda, a birnin Kharkiv da ke gabashin Ukraine, a kalla mutane 12 ne suka jikkata a wani harin baam da Rasha ta kai cikin dare a cewar rundunar 'yan sandan kasar. Sai dai kuma gwamnatin Moscow bata ce komai ba kan hari.