1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Rasha ta kai wa Ukraine kazamin hari

November 17, 2024

Rasha ta kai wa Ukraine hari mafi muni tun bayan barkewar rikici a tsakanin kasashen biyu tare da halaka mutane akalla biyu da kuma lalata cibiyoyin samar da ababen more rayuwa da dama ke da rauni a kasar.

Ukraine-Krieg
Hoto: AP/picture alliance

Rasha ta kai wa Ukraine wasu jerin hare-hare da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka a safiyar wannan Lahadi, lamarin da ya yi ajalin mutane akalla biyu tare da lalata cibiyoyin samar da makamashi da dama a fadin kasar.

Kamfanin sarrafa makamashi na kasar Ukraine DTEK ya ba da rahoton cewa harin ya yi sanadin lalacewar darurruwan na'urori, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a wasu sannan kasar ciki har da birnin Kiev fadar gwamnati.  

Ministan harkokin wajen Ukraine ya yi tir da harin da ya bayyana a matsayin mafi muni da Rasha ke kai wa kasarsa, wanda ke zuwa a daidai lokacin da sojojin Kiev ke fama da matsaloli a fagen daga tare kuma da fargabar katsewar tallafin da Amurka ke bai wa kasar bayan nasar Trump.

Duk da cewa har yanzu ba a kai kammala fitar da kididdigar barnar da harin ya haddasa ba, amma Shugaba Zelensky ya ce sojojin kasar sun yi nasarar kakkabo akalla makamai guda 140 daga wadanda Rashar ta harba.