Rasha ta kai wani hari mai muni a Ukraine
October 9, 2022Talla
Labarin sabon harin ya zo ne kwana guda bayan karya wani bangare na wata gadar da ta hada kasashen biyu, yankin da Rasha ke matukar amfani da shi wajen safarar makamai zuwa Ukraine.
Harin na wannan Lahadin ya kuma jikkata mutane 49 ciki har da kananan yara.
Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine, ya bayyana harin wanda shi ne mafi muni da aka gani a yankin a baya-bayan nan, a matsayin wata babbar mugunta.
A ranar Litinin ne Shugaba Putin na Rasha, zai jagoranci majalisar tsaron kasar, wanda zai duba batun da ya shafi karyewar gadar mai muhimmanci ga Rasha a yakin.
Ko a farkon wannan makon ma wani harin ya yi sanadiyyar rayukan mutane 17 a yankin na Zaporizhzhia wanda Rasha ke da'awar kwacewa cikin yankuna hudu na Ukraine.