1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rasha ta ziyarci shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar

December 4, 2023

Wata tawagar jami’an gwamnatin Rasha ta soma wata ziyarar aiki a Jamhuriyar Nijar inda suka gana da shugaban hukumar mulkin sojan kasar Janar Abdourahmane Tchiani a fadarsa.

Hoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Wata tawagar manyan jami'an gwamnatin kasar Rasha ta soma wata ziyarar aiki a kasar jamhuriyar Nijar da rahotanni ke cewa tuni ta gana da shugaban hukumar mulkin sojan kasar Janar Abdourahmane Tchiani a fadarsa dake birnin Yamai.

Tawagar manyan jami'an gwamnatin kasar ta Rasha ta iso ne da yammacin lahadi 3 gawatan Disambar 2023, karkashin jagorancin karamin ministan tsaron kasar ta Rasha Janar Evkourov Lunus-Bek.

A hakumance dai ba a sanar da makasudin zuwan wannan tawaga ba a Nijar, illa dai kawai an bayyana cewa za ta yi taro da hukumomin tsaro na kasar ta Nijar.

Sai dai wani abun lura shi ne a daidai lokacin da tawagar jami'an kasar ta Rasha ke shirin zuwa Nijar, sabuwar jakadiyar kasar Amirka wacce ke a kasar ta Nijar tun a watan Agustan da ya gabata ta zabura  a karon farko zuwa ganawa da hukumomin kasar ta Nijar tare da gabatar da takardarta ta kama aiki.

Malam Bana Ibrahim, wani dan fafutika mai goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki fassara rububin zawarcin nijar da kasashen biyu na Amirka da Rasha ke a yi a matsayin wata alama ta samun cikakken ‘yancin Nijar a yanzu

Shi ma dai Parfesa Dicko Abdoulaye mai sharhi kan harkokin tsaro da siyasa a Nijar fassara lamarin ya yi da wata babbar nasara ga kasar Rasha, nasarar da amma ya ce na iya barin baya da kura musamman a fannin huldar nijar da Amirka a nan gaba.

 Wannan shi ne karo na farko da wata tawagar jami'an gwamnatin kasar ta Rasha ke kai ziyara a kasar ta Nijar din tun bayan juyin mulki a kasar.