1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rasha ta kakkabo jiragen Ukraine marasa matuka

October 8, 2024

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta yi nasarar kakkabo jiragen Ukraine marasa matuka kimanin 16 a kan iyakar kasar da Bahar Aswad, tare kuma da tarwatsa dukkan jiragen da ke shawagi a sararin samaniya.

Wani sojan Rasha da yake sarrafa jirgi mara matuki a yankin Lugansk na Rasha
Wani sojan Rasha da yake sarrafa jirgi mara matuki a yankin Lugansk na RashaHoto: Alexander Reka/ITAR-TASS/IMAGO

Rasha ta ce 14 daga cikin jiragen marasa matuka ta kakkabo su ne a lardin Belgorod da ke kan iyakar kasar ta Rasha da Ukraine, yayin da biyu suka fada tekun Bahar Aswad, a cewar ma'aikatar tsaron Rasha a wani sako da ta wallafa a shafin Telegram.

Karin bayani: Rasha ta kai hari babban birnin Ukraine, Kyiv

Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ke cewa tana taba-alli da Kungiyar Tsaro ta NATO a wani taron gaggawa da zasu gudanar duk da cewa taron bai da nasaba da rage tasirin farmakin da ta ke yi ba a Ukraine, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Rasha RIA ta rawaito jawabin Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Rasha Alexander Grushko a fadar Kremlin.