1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kammala janye sojoji daga Kherson

Abdullahi Tanko Bala
November 11, 2022

Janyewa daga Kherson na zama babbar koma baya ga Rasha kasancewar Kherson babban birni daya tilo da ya fada hannun Rasha a farkon barkewar yakin

Ukraine Krieg | Rückeroberung von Cherson
Hoto: Celestino Arce/NurPhoto/picture alliance

Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa ta kammala janye dukkan sojojinta daga kudancin birnin Kherson.

A sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce babu wani kayan sojanta ko makami kwaya daya da ta bari a baya.

Janyewar sojojin dai wata babbar koma baya ce ga sojojin Rasha kasancewar Kherson shi ne kadai babban birnin Ukraine da ya fada hannun Rasha a lokacin da aka fara yakin. Sannan kuma yankin muhimmin mashigi ne zuwa yankin tsibirin Crimea wanda Rasha ta shigar cikin kasarta a shekarar 2014