1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Rasha ta kwace iko da wasu garuruwa a Ukraine

May 12, 2024

Sojojin Rasha na ci gaba da matsa lamba a farmakin da suka kaddamar a yankin Kharkiv da ke arewacin Ukraine inda suka yi ikirarin kwace iko da wasu garuruwa da ke kusa da kan iyaka.

Russen treffen Charkiw nachts mit S-300-Raketen
Hoto: Vyacheslav Madiyevskyy/Ukrinform/IMAGO

Rasha ta ce sojojinta sun kara samun galaba a yankin Kharkiv da ke arewacin Ukraine tare da yin ikirarin kwace iko da wasu garuruwa hudu da ke kusa da kan iyaka a farmakin da ta kaddamar a ranar Juma'a wanda ya tilastawa dubban mutane tserewa daga yankin. 

Karin bayani: Rasha ta kwace iko da Bogdanivka na Ukraine

Gwamnan yakin Oleg Synegubov ya tabbatar da hakan a shafinsa na X, inda ya ce an kwashe sama da mutane dubu hudu daga yankin kwana guda bayan da dakarun Moscow suka yi ikirarin kwace iko da garuruwa biyar.

Wani jami'in 'yan sandan Ukraine ya shadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa fararen hula da dama sun mutu a yankin sakamakon ruwan bama-bamai da dakarun Rashar suka yi a jiya Asabar.

Karin bayani: Ukraine ta bukaci agajin kawayenta cikin gaggawa

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce sabbin garuruwan da suka dawo karkashin ikonta sun hadar da Gatichtché da Krasnoïé da Morokhovets da kuma Oleïnikovo kuma sojojinta na ci gaba da matsa lamba a wannan yanki da birni na biyu mafi girma a Ukraine ya ke.