Kasar Rasha tamayar wa da Trump martani
July 12, 2018Talla
Ya kuma kara da cewar shimfida bututun da ke kai wa Jamus iskar gas daga Rasha kai tsaye ya samo asali ne sakamakon yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen biyu.
A halin yanzu alamu sun yi nuni da cewar ganawar da shugaba Vladimir Putin na Rasha zai yi da Donald Trump a ranar Litinin mai zuwa ba za ta haifar da 'da mai ido ba sakamakon kamarin da rashin jituwar kasashen biyu ke ci gaba da yi daidai lokacin da Donald Trump ke ci gaba da fuskantar Allah wadai daga wasu kasashen na Tarayyar Turai sakamakon kutse cikin al'amuran gudanarwa kasashen da suka dade suna kawance da Amirka.