SiyasaTurai
Rasha ba ta sake kwace yanki a Ukraine ba
April 2, 2026
Talla
Rahoton ya ce wannan shi ne karon farko cikin shekaru biyu da rabi da sojojin Moscow suka gaza samun nasara a yunkurin fadada yankunan da suke kwacewa a Ukraine.
Binciken ya ce nasarar sojojin Rasha ya ragu tun karshen shekarar 2025, sakamakon ciagaba da Ukraine ta samu a Kudu maso gabashin kasar, tare da asarar wasu yankuna a watan Fabrairu da Maris na shekarar 2026 musamman yadda ta rasa yankunan Donetsk da Dnipropetrovsk.
Bayanai na cewa a dai-dai lokacin da Shugaban kasar Ukraine din Volodymyr Zelensky ya kulla yarjejeniyar tsaro da wasu kasashen Larabawa na yankin Gulf, sojojin kasar sun sake kwato kimanin murabba'in kilomita tara a watan Maris da ta gabata.