Rasha ta kori jami'an gwamnatin Jamus
December 12, 2019Talla
A wani mataki na ramuwar gayya gwamnatin Moscow ta ba wa jami'an diflomasiyya na Jamus biyu wa'adin kwanki bakwai su bar kasar, bayan korar nata jami'an a Berlin kan zargin kisan wani tsohon kwamandan sojin kasar Jojiya.
A makon jiya ne kasashen Rasha da Jamus suka fara sa-in-sa bayan Jamus ta zargi Moscow da hannu a kisan wani tsohon kwamandan sojin kasar jojiya a wurin shakatawa a birnin Berlin.