1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kori jami'an diplomasiyyar Jamus

Binta Aliyu Zurmi
April 22, 2023

A wani mataki na ramuwar gayya, Rasha ta kori jami'an diplosmasiyyar Jamus sama da 20 a cewar mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rasha.

Russland EU-Länder weisen russische Diplomaten wegen Vergiftung durch Ex-Spion Skripal aus
Hoto: Sefa Karacan/AA/picture alliance

Wannan matakin na zuwa ne bayan da Rasha ta sha alwashin mayar wa Berlin da martani mai zafi a game da matakin da ta dauka na korar jami'an diflomassiyarta, fadar Kremlin ta ce korar jami'anta ba zai taba yin wani tasiri ba illa ya kara dagula lamura a dangantakarsu. 

Kyakyawar dangantakar da ke a tsakanin kasashen biyu ta soma tsami, tun bayan da Rashan ta soma mamayar Ukraine a bara, kuma kasancewar Jamus a sahun gaban kasashen yamma da ke goyon bayan Ukraine, lamarin ya shafi huldarsu ta fuskar kasuwanci musanman kan batun makamashin gas.