1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kwace iko da Avdiivka na Ukraine

February 18, 2024

Rasha ta yi ikirarin kwace iko da garin Avdiivka bayan da dakarun Ukraine suka janye daga garin.

Ukraine, Awdijiwka | ukrainische Soldaten
Hoto: Elif Kizil/Anadolu/picture alliance

Ukraine ta ce ta janye dakarunta ne domin ta tseratar da rayuwarsu bayan kwashe watanni ana gwabza kazamin fada. Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya ce wannan nasara ce a gare su, inda ya jinjina wa dakarunsa.

Rasha ta ce har yanzu akwai sauran dakarun Ukraine da suka boye a yankin na Avdiivka da ke kasancewa wani bangare a manufar Rasha na samun cikakken iko da yankin Donbas.

Kafar talabijin ta Rasha ta nuna yadda aka daga tutar kasar sama bayan sauke ta Ukraine. A nata bangaren, Ukraine ta ce ba a samu asarar rayuka ba, sai dai kuma al'amura sun daidaita a garin tun bayan da ta janye.