SiyasaTurai
Rasha ta mika gawarwakin dakarun Kiev 1,000 ga Ukraine
July 17, 2025
Talla
Babban Jami'in Rasha da ke shiga tsakani Vladimir Medinsky, shi ne ya sanar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafin Telegram wanda kuma aka yada a sauran shafukan sada zumunta.
Karin bayani: Amurka za ta kara wa Ukraine karfin yaki da Rasha
Kazalika fadar Kreamlin ta sanar da cewa ta karbi gawarwarkin dakarunta 19 da suka mutu daga hannun gwamnatin Ukriane duk dai domin fara aiwatar da yarjejeniyar sulhu a tsakanin kasashen da basa ga maciji da juna.
Karin bayani: Trump ya yi alkawarin ba wa Ukraine karin makamai
Ga dukkan alamu dai Rasha da Ukraine basu da burin kawo karshen yakin da suka gwabzawa a nan kusa, duk da matsin lamba na bukatar tsagaita bude wuta daga shugaban Amurka Donald Trump.