1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Rasha na son ganin an karfafa yarjejeniyar nukiliyar Iran

Ramatu Garba Baba
March 9, 2021

Gwamnatin Rasha ta yi kira ga Amurka da Iran da su dauki matakin sulhu don shawo kan sabanin da aka samu a game da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015.

Österreich Wien | Internationale Atomenergie-Organisation
Hoto: picture-alliance/Xinhua News Agency/IAEA/D. Calma

Da yake bayani a yayin wata ziyara da ya kai Hadaddiyar Daular Larabawa, Ministan harkokin wajen Rashan, Sergei Lavrov, ya ce kwan-gaba kwan-bayan da ke a tsakanin kasashen biyu, zai sa a jima ba a warware matsalar da ta hana ci gaba da aiki da yarjejeniyar ba, ya ce lokaci ya yi da za a dora daga inda aka tsaya don cimma manufar shirin.

Takaita sa ido dai kan cibiyoyin nukiliyar Iran na cikin yarjejeniyar da kasashen duniyan suka cimma a 2015 a birnin Vienna, matakin da ya takawa Iran din birki daga gina tashoshin nukiliya a matsayin makami. Sai dai janyewar Amirka daga yajejeniyar a yayin mulkin Donald Trump, ya fusata Iran fara karya ka'idojin.