1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta nemi ahuwa bayan harbe jirgin Azerbaijan

December 28, 2024

Shugaban kasar Rasha ya bukaci ahuwa daga gwamnatin kasar Azerbaijan, tare da daukar alhakin harbe jirgin saman fasinjan nan da ya fada a Kazakhstan a tsakiyar makon nan.

Shugaban Rasha, Vladimir Putin
Shugaba Vladimir Putin na kasar RashaHoto: Russian President Press Office/dpa/picture alliance

Shugaba Putin na kasar Rasha ya nemi gafara daga shugaban kasar Azerbeijan, bayan faduwar da jirgin saman Azerbaijan ya yi a Kazakhstan, hadarin kuma da ya yi sanadin mutuwar mutane 38 a ranar Laraba.

Shugaba Putin ya bayyana hadarin da ya auku a sararin samaniyar Rasha da wani lamari mai muni kwarai.

Ahuwar ta Rasha ga Azerbaijan dai ta fito ne daga wata tattaunawa ta wayar tarho da shugabannin biyu suka yi da ranar yau Asabar.

Shugaba Vladimir Putin ya ce an samu kuskure ne daga ayyukan da sojojin sama na kasarsa ke yi na martani ga wasu jirage marasa matuka mallakin Ukraine.

Jirgin fasinjan na Azerbaijan dai ya taso ne daga birnin Baku zuwa Grozny babban birnin Jamhuriyar Chechnya.