1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta sake kai farmaki kan Ukraine

Abdul-raheem Hassan
November 29, 2025

Dakarun Rasha sun kaddamar da sabbin hare-hare da jirage mara matuka a wasu yankunan Kiev a cikin dare, mutane biyu sun mutu ciki har da karamin yaro wasu da dama sun jikkata.

Ukraine Kyjiw 2025 | Wohnhäuser brennen nach russischen Raketen- und Drohnenangriffen auf die Hauptstadt
Yadda jiragen yakin Rasha suka yi luguden wuta kan unguwannin Kyiv cikin dareHoto: Anton Shynkarenko/REUTERS

Harin an kai shi ne da makamai masu linzami da jirage marasa matuka, inda suka lalata wasu gidaje da gine-gine a gundumomi daban-daban. A baya-bayan nan birnin Kiev na yawan fuskantar hare-haren jiragen sama na yakin Rasha mafiya muni wanda ke shafar tashoshin makashin kasar.

Ukraine na kare kanta daga mamayar da kasar Rasha ta fara tun a watan Fabrairun 2022, tare da gagarumin tallafi daga kasahen Yamma. Sai dai sabon farmakin ya zo ne yayin da ake sa ran tawagar Amurka za ta je birnin Moscow domin tattaunawa da Vladimir Putin kan shirin kawo karshen yakin wanda Shugaba Donald Trump ya gabatar mai dauke da shawarwari 28.

Daftarin shawarwarin guda 28, ana ganin ya ba wa Rasha fifiko ciki har da neman Ukraine ta hakura da wasu yankuna da Rasha ta kwace da rage yawan sojoji da janye batun shiga kungiyar tsaro ta NATO.

Shugabannin Turai na gaba gaba don ganin an cimma yarjejeniyar, bayan nuna fargabar makomar tsaron yakina nuna fargabar cewa yankunansu na cikin barazanar tsaro daga Rasha a nan gaba.