Rasha ta tsinke hulda sayar da gas da Jamus
May 12, 2022Talla
Shugaban Rashar Vladmir Putin ya ba da umarnin haramta yin kasuwanci da kafanonin na Jamus wanda ya ce bai kamata a ci gaba da yin kasuwancin iskan gas din da su ba. An sanya Gazprom reshen Germany ƙarƙashin ikon gwamnatin Jamus a farkon watan Afrilu da ya gabata. A halin da ake ciki gwamnatin Jamus ta jaddada cewar tana da wadataccen iskan gas kawo yanzu, sannan ta ce babu abin tayar da hankali a ciki.