1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta soke shirinta na saida wa Iran makamai

September 22, 2010

Rasha ta yanke hukunci dakatar da saida makamai ga Iran sakamakon takunkumin Majalisar Ɗinkin Duniya

Rasha ta dakatar da shirin saida makamai ga IranHoto: AP

Ƙasar Rasha ta soke shirinta na bai wa  Iran sababbin makaman S-300 sakamakon takunkumin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙagabawa ƙasar ta Teheran. Wani babban jami'in sojin Rasha Nicolai Makarov ya ce yin hakan zai karya wannan takunkumi. Wannan ne karo na farko da babban Jami'i daga ƙasar Rasha zai tabbatar da cewa an soke wannan shirin da ya daɗe ya na ciwa ƙasashen Amirka da Israela tuwo a ƙwarya.

Makamin na S 300 za a iya amfani da shi daga nesa a gano ƙananan jiragen yaƙi masu tashi  ƙasa-kasa a kuma hallaka su.

Da farko, ministan harkokin wajen Rasha ya ce ba abun da zai hana su bai wa ƙasar Iran makaman tunda makaman kare kai ne ba wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya wa takunkumi ba.

Mawallafi: Pinaɗo Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi