Rasha ta yi tir da takunkuman EU a kan Kirimiya
December 18, 2014Talla
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce sabbin takunkuman Kungiyar Tarayyar Turai, da suka haramta zuba jari a yankin Kirimiya ba abin karbuwa ba ne ko kadan, kuma wariya ne aka nuna wa yankin na tsibirin tekun Bahar Aswad wanda Mosko ta mayar karkashinta a cikin wata Maris. A cikin wata sanarwa ma'aikatar ta ce kamata ya yi EU mai shalkwata a birnin Brussels ta san cewa ba za a iya raba yankunan Kirimiya da Sebastopol da Rasha ba.
A wannan Alhamis Kungiyar Tarayyar Turai ta sanya takunkumin hana zuba jari a yankin Krimiya, musamman a fannonin samar da makamashi da mai da iskar gas da kuma harkokin sufuri da na sadarwa. Sannan za a hana jiragen ruwan Tarayyar Turai bi ta tekun Bahar Aswad. A ranar Asabar sabbin takunkuman za su fara aiki.