1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Rasha ta yi wa Burtaniya barazana kan Ukraine

May 6, 2024

Rasha ta yi barazanar kai wa cibiyoyi da kayan aikin sojan Burtaniya da ke Ukraine hari, muddin sojojin Kiev suka yi amfani da wadannan wurare da kuma makaman da London ta ba su domin kai mata hari.

Rasha ta yi wa Burtaniya barazana kan Ukraine
Rasha ta yi wa Burtaniya barazana kan UkraineHoto: Vyacheslav Prokofyev/TASS/dpa/picture alliance

Barazanar ta Moscow na zuwa ne a daidai lokacin da ta kira jakadan Burtaniya da na Faransa jim kadan bayan wani furuci da ministan harkokin wajen Burtaniyar David Cameron ya yi, inda ya ce Ukraine za ta iya yin amfani da makaman da London ta bata domin kai wa Rasha hare-hare.

Karin bayani: Burtaniya za ta tura wa Ukraine motocin sulke

A cewar ma'aikatar harkokin wajen Rasha kalaman na David Cameron sun saba wa alkawarin da Burtaniya ta yi cewa Ukraine ba za ta yi amfani da wadannan makamai ba domin kai hari a wani yanki na kasar ba.

Tuni ma dai shugaba Putin ya ba da umurnin fara wani atisayen makaman nukiliya a matsayin martani ga kalaman na David Cameron da kuma wasu kalamai na takala da ya ce shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kan yiwuwar aike wa da sojojin NATO zuwa fagen daga a Ukraine.