Rasha ta yi wa 'yan tawayen Siriya tayin ficewa daga Alepo
October 13, 2016A kasar Siriya a daidai lokacin da jiragen yakin gwamnatin kasar da na Rasha ke ci gaba da lugudan wuta kan birnin Alepo, kasar Rasha ta ce a shirye take ta bayar da kareya ga mayakan 'yan tawayen da ke bukatar ficewa daga birnin.
Janar Serguei Roudskoi daya daga cikin shugabannin sojojin rashar ne dai ya sanar da hakan a wannan Alhamis inda ya ce a shirye kuma amince da ficewar fararan hula daga yankin gabashin Alepo dama shigar da kayan agaji a cikin unguwannin 'yan tawayen wadanda sojojin Bachar al-Assad ke kokarin maido da su a karkashin ikonsu.
Wanan tayi na kasar Rasha ya zo a daidai lokacin da kasashen Amirka da Rasha ke shirin gudanar da wasu taruka tare da hadin gwiwar kasashen Larabawa da na Turai a biranen Lusanne da London a karshen mako da nufin sake cimma wata yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin na Alepo