1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rasha ta yi watsi da tayin Amurka

Binta Aliyu Zurmi
January 18, 2024

Ministan harkokin kasashen ketare na Rasha Sergey Lavrov ya yi watsi da tayin Amurka na komawa kan teburin tattaunawa a kan batun mallakar makamashin nukiliya.

Moskau Außenminister Lawrow
Hoto: Alexander Shcherbak/Tass/IMAGO

Lavrov ya ce hakan ba zai yiwu ba muddin Amurka da kawayenta na ci gaba da goya wa Ukraine baya da ma ba ta makamai a yakin da suke yi.

Da yake jawabi a taronsu na shekara-shekara, Lavrov ya zargi kasashen yamma da rura wutar rikici a duniya da ma ingiza Ukraine. 

Babban jami'in diplomasiyyar Rashar, ya ce akwai bukatar Amurka ta sauka daga matakin da ta hau a kan kasarsa idan har tana neman wani sulhu da su.

A cewarsa Rasha ba ta yi wa kasashen yamma barazana da makamin na nukiliya ba, ya kuma gargadi kasashen Amurka da kawayenta da kada su kuskura su yi musu wannan barazanar.

Dangantaka tsakanin Rasha da kasashen yamma dai ta jima da yin tsami tun bayan da ta kaddamar da mamaya a kan Ukraine a Fabrairun shekarar 2022.

Karin bayani: Cacar-baka ta barke a tsakanin Rasha da kasashen yamma