1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta zargi Ukraine da harin cibiyar nukiliya

August 30, 2022

Rasha da Ukraine sun dauki lokaci suna zargin juna da kai hari a cibiyar ta Zaporizhzhia da ke zama babbar cibiyar makamashin nukiliya a nahiyra Turai, wadda kuma fashewarta ka iya haddasa gagarumar annoba ga duniya.

Ukraine | Atomkraftwerk Saporischschja
Hoto: Alexander Ermochenko/REUTERS

Wakilan gwamnatin Rasha da ke iko da garin Enerhodar da ke cikin Ukraine sun zargi dakarun Ukraine da sake kai hari a kusa da cibiyar nukiliya ta Zaporizhzhia. 

A sanarwar da suka fitar a safiyar talatar nan, jami'an na Rasha sun ce hare-hare guda biyu Ukraine ta kai kusa da bangaren mai na cibiyar nukiliyar.

A cikin wannan makon hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da makamashin nukiliya za ta ziyarci cibiyar domin gane wa idanunta abin da ke faruwa.