Rasha na zargin Ukraine da kitsa kai hari
October 24, 2022Talla
Harin wanda ya lalata wani gini da ke kusa da Kherson ya zo ne bayan da Rasha ta umurci mazauna yankin su kimanin dubu 60 da su tashi don tsira da rayuwarsa.
Yayin zantawa da takwarorinsa na kasashen Birtaniya da Faransa da kuma Turkiyya ta wayar tarho, ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya yi ikrarin cewa Ukraine na shirin amfani da makami mai guba a kan Rasha.
A cikin wata sanarwar ta hadin gwiwa da suka fitar, kasashen Birtaniya da Faransa da kuma Amirka sun karyata zargin na Rasha.
Shi ma ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya yi watsi da zargin, ya na mai bayyana shi a matsayin mara tushe. Kuleba ya kuma ce a lokuta da dama, Rasha kan zargi wasu bangarori da dukkan abun da ta shirya aikatawa.