1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zargin 'yan Afirka na yaki tare da Rasha

Lateefa Mustapha Ja'afar SB
February 13, 2026

Jaridun na Jamus sun duba tasirin saka 'yan Afirka cikin sojojin Rasha domin fafatawa da Ukraiine, haka zawarcin da Amurka take yi wa kasashe AES na Afirka ta Yamma da sojoji suka yi juyin mulki domin sake kulla hulda.

Shugabannin Rasha da na Afirka
Shugabannin Rasha da na AfirkaHoto: ZDF/DW

Ba mu fara da jaridar Der Tagesspiegel da ta rubuta sharhinta mai taken: "Aikin bogi, 'yan afirka a matsayin sojojin Putin ta hanyar tirsasawa." Jaridar ta ce fargaba da tsoro sun bayyana a fuskar Francis Ndarua dan kasar Kenya, mai shekaru 35 a duniya na sanye da kakin sojojin Rasha. Yana daga cikin dakarun kunar bakin wake a rundunar sojojin Rasha, Ndarua ya bayyana cikin wani faifen bidiyo da babu tabbacin inda aka dauke shi.

Hoton Shugaba Vladimir Putin na RashaHoto: Esa Alexander/REUTERS

Ko har yanzu Ndarua na raye ko kuma ya halaka a harin kunar bakin waken, babu wanda ya sani. Mahaifiyarsa ta ce rabon da ta ji daga gare shi, tun watan Oktoba na 2025. Ba dai shi kadai ba ne, sama da mazaje 1400 daga kasashen Afirka 36 ne ke yaki a Rasha ba da son ransu ba, kamar yadda bayanan da suka fito daga Ukraine suka nunar.

Amurka da kasashen AES

A nata bangaren jaridar Welt online ta rubuta nata sharhin mai taken: "Cibiyar ta'addanci, sabon salo- Mai yasa kwatsam Amurka ta fara haba-haba da gwamnatocin mulkin soja a Afirka? Jaraidar ta ce: Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da mamaki a siyasarsa ta nahiyar Afirka, inda ya lashe amansa a kansu. Bayan shekaru yana nisanta kansa, Washington ta karfafa yin aiki tare da gwamnatocin mulkin soja a yankin Sahel. Da dama sun yi maraba da hakan, yayin da Turai ta kasance mara alkibla a kai.

Jaridar ta ce, har a karshen watan Oktoba akwai tsamin dangantaka tsakanin Mali da Amurka. Gwamnatin Amurkan, ta sanya Mali a cikin kasashen da 'yan kasarsu za su ajiye dala 10,000 kafin a ba su takardar izinin shiga wato visa.  Gwamnatin mulkin soja a Bamako ta mayar da martani nan take, ta hanyar saka nata matakan ga 'yan kasar Amurka.

Jami'in diflomasiyyar Amurka Nick Checker da Abdoulaye Diop ministan harkokin wajen MaliHoto: U.S. Department of State/Bureau of African Affairs/X

Abin mamaki, Shugaba Trump ya lashe amansa ta hanyar cire Mali daga cikin jerin kasashen. Abu ne da bai taka kara ya karya ba, amma a yanzu Amurkan ta tura wakili zuwa Bamako da nufin girmama kasancewar Mali a matsayin kasa da kuma dabbaka sabuwar dangantaka.

Ita kuwa jaridar die tageszeitung ta yi nata sharhin mai taken: Taimakon gaggawa kalilan ga Mosambik, wadda ke fama da ibtila'in ambaliyar ruwa. Daruruwan mutane sun tsere daga gidajensu, a kasar ta Afirka da ke fama da ambaliya. Jamus ta aike kudin da bai taka kara ya karya ba, idan aka yi la'akari da wanda take turawa a irin wannan yanayi ga wasu kasashen.

Rahotannin da die tageszeitung ta samu, sun nunar da cewa Jamus ta tura kimanin Euro 640,000 a tsakiyar watan Disamar shekarar ta 2025 da ta gabata a matsayin tallafi ga dubban mutanen da abin ya shafa da kuma suka yi asarar dukiyoyinsu da gidajensu.

Batun Epstein a nahiyar Afirka

Marigayi Jeffrey Epstein a tsakiya wanda ya yi kaurin suna wajen cin zarafin mataHoto: Uma Sanghvi/Palm Beach Post/AP Photo/picture alliance

Ba mu karkare da wani sharhin na dabam da die tageszeitung din ta rubuta mai taken: "Epstein ya isa gabashin Afirka, Jeffrey Epstein mai cin-zarafi ta hanyar fyade ya yi tattaki zuwa Afirka. An gano ya yi hulda da tsofaffin shugabannin kasa- ya kuma ziyarci Malindi da ke zaman cibiyar yin safarar mutane a Kenya. Jaridar ta ce: Kasashen Kenya da Tanzaniya da Yuganda da Somaliya da Senegal, sun bayyana cikin kundin Epstein da yawansa ya kai kimanin miliyan 300 wanda kuma ya kunshi sakonnnin email da hotuna da ma faya-fayen bidiyo da ma'aikatar shari'a ta Amurka ta fitar makonni biyun da suka gabata.

Mai cin-zarafin ta hanyar fyade Epstein ya yi takakkiya zuwa Afirka sau da dama, kuma ya san manyan mutane da suka hadar da tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da takwaransa na Afirka ta Kudu Jacob Zuma. An ma yi zargin cewa, kusancinsu zai iya kai wa ya samar musu 'yan matan da za su yi mu'amala da su. Yayin wata ziyara da Zuma ya kai birnin London na Birtaniya a watan Maris na 2010, Epstein ya rubuta wasika zuwa ga dan siyasar Birtaniya na jam'iyyar Labour Peter Mandelson cewa: "Mark Lloyd zai gudanar da bikin cin abincin dare ga Zuma gobe da yamma a Ritz, na gayyaci wasu kyawawan 'yan matan Rasha su halarta."

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani