Rasha: 'Yan adawa sun yi zargin magudin zabe
March 18, 2018Talla
Hakazalika Alexei Navalny babban mai hamayya da gwamnatin Putin da aka hana wa yin takara a zaben bisa wasu hujjoji na shari'a, ya wallafa a shafinsa na yanar gizo hotunan bidiyon magudi da ya ce an aikata da akwatunan zabe. Tuni sakamakon zaben ya soma nuna cewa shugaba mai ci Vladimir Putin ke sahun gaba don lashe zaben shugabancin kasar a sabon wa'adin mulki karo na hudu.
Rahotannin na nuni da cewa bayan kidayar kashi saba'in cikin dari na kuri'un da aka kada, shugaba Putin na sahun gaba daga cikin 'yan takara bakwai da suka fafata a kokarin samun nasara dare kujerar mulkin kasar.