Rasha za ta ci gaba da rufe gas dinta
September 2, 2022Talla
Kamfanin samar da iskar gas mallakin Rasha wato Gazprom, ya ce bututun samar da makamashinsa na Nord Stream 1 zai ci gaba da zama a rufe har sai illa Ma Sha Allahu.
Matakin a cewar Gazprom, ya zo ne bayan samun daya daga cikin injunan kamfanin a kusa da St. Petersburg na yoyo.
A cewar kamfanin na Rasha wanda kasashen Turai ke dogaro kan makamashin da yake samarwa, za a ci gaba da rufe bututun ne domin gano yadda zai maganta tsiyayar da iskar ke yi.
Da ma dai a ranar Asabar ne aka tsara dawo da aika makamashin ta bututun na Nord Stream 1, bayan tsaikon kwanaki uku da aka sanar domin bayar da damar gyara.