1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Rasha da kasashen Afirka

Zainab Mohammed Abubakar
July 27, 2023

A taronsu karo na biyu, Rasha na shirin inganta hadin gwiwa da kasashen Afirka. Taron na St. Petersburg zai mayar da hankali kan isar da hatsi da takin zamani zuwa nahiyar.

Afrikanische Delegation zu Besuch in Russland
Hoto: AP

Kwanaki goma da suka gabata, Rasha ta ki tsawaita  yarjejeniyar tsawon shekara na  ba da damar fitar da  kusan tan miliyan 33 na hatsin Ukraine da sauran kayayyakin abinci ta tekun Bahar Maliya.

Rashar dai ta fuskanci suka daga kasashen duniya kan yadda ta hana fitar da alkama da masara masu yawa na Ukraine zuwa kasuwannin duniya, ya na haifar da abinci farashin tashi.

Hatsin da kasashen biyu ke nomawa dai yana da mahimmanci wajen taimakawa yaki da yunwa duniya. Bayan batun samar da abinci, da ana kuma sa ran taron zai tattauna batun fadada harkokin kasuwanci. Rasha ce babbar kasa mai samar da makamai zuwa Afirka.