1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha za ta hau kujerar na ƙi akan rikicin Siriya

February 1, 2012

Rasha ta ce ba za ta bada goyon baya ga ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Siriya ba. har sai an cire yiwuwar amfani da ƙarfin soji don kawo ƙarshen rikicin.

The members of the United Nations Security Council raise their hands to vote, Thursday, Sept. 24, 2009. (AP Photo/Richard Drew)
Kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin DuniyaHoto: AP

Ƙasar Rasha ta nuna alamar cewa za ta hau kujerar na ƙi akan daftarin ƙudirin kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ya buƙaci shugaban ƙasar Siriya Bashar al-Assad ya sauka daga karagar mulki. Rasha ta ce ba za ta amince da daftarin ba, har sai an fayyace ƙarara cewa ba za'a yiwa ƙasar shigar burtu da ƙarfin soji domin kawo ƙarshen zubar da jinin dake faruwa sakamakon zanga zangar adawa da gwamnatin Assad ba. A wannan makon masu rajin kare haƙƙin bil Adama sun ce ƙaruwar tarzoma a Siriyar ta haddasa mutuwar dubban jama'a a Damascus da biranen Hama da Homs da kuma Deraa suka ce sojojin Assad sune ke da alhakin hakan. A ranar Talata ƙasashen larabawa da na yammacin Turai sun yi ta matsin lamba akan kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya gaggauta zartar da ƙudiri ta buƙatar Assad ya sauka ya kuma miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa domin kawo ƙarshen tarzomar ta watanni goma sha ɗaya.

Sai dai kuma kasashen Rasha da China waɗanda dukkaninsu ke da wakilcin dundundun a kwamitin sulhun sun ƙi nuna goyon baya ga daftarin suna masu cewa ba za su amince da shirin sauyin gwamnati ko kuma matakin soji akan ƙasar ba kamar yadda jakadan Rasha a Majalisar Ɗinkin Duniyar Tschurkin ya baiyana " Yace kwamitin sulhu ba shine zai tsarawa ƙasar Siriya yadda za ta shawo kan al'amuranta na cikin gida ba, wannan baya daga cikin dokokin majalisar, a saboda haka bama son kwamitin sulhun ya faɗa cikin wannan tarko domin idan aka fara to kuwa zai wuya a dakatar da wannan hali".

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mohammed Nasiru Awal