Rasha za ta janye sojoji daga Siriya
December 11, 2017Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayar da umurnin kwashe mafiyawancin sojojin kasarsa da ke a kasar Siriya zuwa gida. Ya sanar da hakan ne a lokacin wata ziyarar ba zata da ya kai a wannan Litinin a cibiyar sojoji ta Hmeimin inda sojojin Rashar ke girke.
Kamfanin dillancin labaran kasar ta Rasha na Interfax ya ruwaito Shugaba Putin din na cewa a tsawon shekaru biyu da suka gabata sojojin Rashar tare da takwarorinsu an Siriya sun yi nasarar karya lagon kungiyoyin 'yan ta'adda, a dan haka ne a yanzu ya dauki wannan mataki na mayar da akasarin sojojin Rashar zuwa gida.
Shugaban kasar ta Siriya Bashar al-Assad da ministan tsaron kasar Rasha Serguei Choigou da babban kwamandan sojojin Rasha a Siriya Janar Serguei Sourovikine ne suka tarbi Shugaba Putin a ziyarar ba zatar da ya kai a barikin sojojin ta Hmeimin.