1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha za ta kai harin ramuwar gayya a Kyiv

Abdullahi Tanko Bala
April 15, 2022

Rasha ta kai hari kan wani kamfani kera makamai masu linzami a kusa da birnin Kyiv wadanda Ukraine ta ce ta yi amfani da su wajen nutsar da jirgin ruwan Rasha

Ukraine-Krieg - Kiew
Hoto: Mykhaylo Palinchak/SOPA/ZUMA/picture alliance

Harin da Rasha ta kai ya lalata wani ginin ofisoshi a tashar Vizar da ke kusa da babban filin jirgin saman Zhuliany a Ukraine. Tun da farko Rasha ta sanar da cewa ta yi amfani da makamai masu linzami daga tashar jirgin ruwa wajen kai harin.

A wani labarin kuma Rasha ta umarci jami'an diflomasiyya na kungiyar tarayyar Turai su 18 da ke zaune a cikin kasarta da su tattara ya nasu ya nasu su bar kasar.

A cikin wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar, ta ce jakadun18 ba a bukatar su a cikin kasar kuma wajibi su tattara ya nasu ya nasu su fice daga kasar Rasha nan  ba da jimawa ba.

Matakin na zuwa ne bayan da kungiyar tarayyar Turai ta umarci jami'an diflomasiyyar Rasha 19 su bar EU a ranar 5 ga wannan watan na Afrilu.
 
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce ta aika sammaci ga Jakadan kungiyar tarayyar Turai a Rasha Markus Ederer domin sanar da matakin ramuwar gayya da ta dauka.

Sanarwar ta ce Kungiyar tarayyar Turai ita ce ke da alhakin tabarbarewar dangantakar diflomasiyyar da suka kulla tsawon shekaru da dama.

Kungiyar tarayyar Turan dai ta soki matakin korar jami'an diflomasiyyarta da Rasha ta yi da cewa bai dace ba kuma babu wata hujja ta yin hakan.