1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha za ta koma gasar Olympic

Abdourahamane Hassane
July 7, 2026

Fiye da shekaru huɗu bayan mamayar Rasha a Ukraine, kwamitin tsara wasannin Olympic IOC ya ɗage wasu daga cikin takunkumin da aka sanya wa 'yan wasan Rasha.

Russland Moskau 2018 | Olympische Winterspiele Pyeongchang | Russische Eiskunstläufer am Flughafen
Hoto: Ivan Pisarenko/TASS/IMAGO

'Yan wasan na Rasha dai za su iya cimma burin shiga gasar Olympics ta Los Angeles  na 2028 ko da a wasannin rukuni, sabanin kasar  Belarus, waɗa aka mayar da ita gaba ɗaya a farkon watan Mayu.

 'Yan Rasha ba za su sake samun taken yabo na tutarsu ba nan take, kuma za a ƙara saka ido kan hana shan ƙwayoyi, kara kuzari inji kwamitin na IOC.

Sai dai tun farkon watan Disamba, kwamitin zartarswa naIOC ya ba da shawarar dawo da 'yan Rasha da Belarus tare da waƙoƙi na taken daga tutocin kasahensu a gasar matasa.