1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rasha za ta taimaka wa kasar Indiya

April 28, 2021

Kasar Rasha ta yi wani yunkuri game da agaza wa kasar Indiya da ke fama da taskun annobar corona, inda take ci gaba da asarar rayukan 'ya'yanta kullum ranar Allah Ta'ala.

Russland l Putin leitet Konferenz des Sicherheitsrates
Shugaba Vladimir Putin na kasar RashaHoto: Alexei Druzhinin/AP/picture alliance

Rasha za ta aika da tallafinta na ceto zuwa Indiya, kasar da ke fama da ta'adin annobar corona a halin yanzu, kamar yadda fadar Kremlin ta tabbatar, bayan wata tattaunawar talho da ta wakana tsakanin Shugaba Putin da Firaminista Narendra Modi na Indiya.

Daga cikin kayayyakin da Shugaba Putin na Rasha ya yi wa Indiya alkawari, sun hada da injunan sarrafa iskar oxygen da masu taimaka wa numfashi wato ventilators da wasu magungunan kashen kwayoyin cuta nau'in virus akalla dubu 200.

Indiya ta kasance kasar kasance a kan a duniya wajen fuskantar tsanani na annobar ta corona, inda sama da mutum dubu uku suka mutu a yau kadai, wasu sama da dubu 360 kuwa su ne sabbin kamuwa duk dai a yau din.

Wannan dai adadi ne da ba a taba ganin irin sa ba tun bayan bullar annobar a duniya a farkon shekarar da ta gabata.