Rasha zata tabbatar da ´yancin ´yan jarida, inji shugaba Putin
October 11, 2006Talla
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi alkawarin cewa kasarsa zata tabbatar da ´yancin ´yan jarida. A cikin hira da tashar telebijin ta Jamus ta yi da shi shugaba Putin ya ce yanzu a Rasha ana samar da wata al´uma ce mai nesanta kanta tare da kyamar mulkin kama-karya, amma ta na maraba da mulki irin na demukiradiya. A game da kisan gillan da aka yiwa sananniyar ´yar jaridar kasar mai sukar lamirin gwamnati, wato Anna Polit-Kovskaya, Putin ya jaddada cewa zai bari a gudanar da cikakken bincike don gano wadanda ke da hannu a wannan aika-aika. Bayan tattaunawar da yayi da SGJ Angela Merkel a birnin Dresden, a yau shugaban na Rasha zai gana da Firimiyan jihar Bavariya Edmund Stoiber da wakilan manyan kamfanonin Jamus a birnin Munich.