1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure mai sukar fadar Kremlin

Abdullahi Tanko Bala
April 17, 2023

Kotu a Rasha ta yanke wa Vladimir Kara-Murza da ya yi kaurin suna wajen sukar fadar Kremlin daukrin shekaru 25 a gidan yari bisa samun sa da laifin cin amanar kasa.

Vladimir Kara-Murza
Hoto: Dmitry Serebryakov/AP/picture alliance

Mai shekaru 41 Kara-Murza ya soki mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, ya kuma nanata wa kotun cewa yana nan a kan bakarsa.

Ya rika furta kalamai yana cewa Rasha za sami 'yanci a lokacin da kotun ta ke yanke masa hukunci.

Wannan dai shi ne hukunci mafi tsauri da aka yanke tun bayan da Rasha ta kafa dokar hana sukar rundunar sojin kasar wanda ta baiyana a matsayin babban laifi bayan da kasar ta afkawa Ukraine a watan Fabrairun 2022.

Lauyan sa ya shaida wa tashar DW cewa bisa la'akari da yanayin lafiyar Kara-Murza wannan tamkar hukuncin kisa ne aka yanke masa.

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta tir da hukuncin wanda ta ce ya nuna kololuwar tursasawa da Rasha ke yi.